Saturday, 23 September 2017

Gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar da rahoto kan inganta rayuwar al'umma ga majalisar dinkin Duniya

Mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya Amina Muhammad kenan tare da mataimakin gwamnan jihar Kaduna Bala Bantex a lokacin da yake mika rahoton gwamnatin jiharshi na habbaka cigaban rayuwa da samarwa mutane abubuwan more rayuwa na majalisar dinkun Duniya ga majalisar.

 Rahoton dai yayi bayanine akan yanda gwamnatin jihar Kaduna zata bayar da gudummuwa wajen ganin an cimma wannan burin na majalisar Dinkin Duniya cikin lokaci, wasu daga ciki abinda wannan shiri ya kunsa sun hada da samarwa da mutane abinci me gina jiki da abubuwan kula da lafiya da kowa zai iya amfana dashi da samar da yanayin muhalli me kyau da inganta harkar noma dadai sauransu.No comments:

Post a Comment