Friday, 15 September 2017

Hadiza Gabon ta ba masoyanta kyautar katin waya na Naira Dubu Goma

Shahararriyar jarumar fim din Hausa, Hadiza Gabon ta bayar da kyautar katin waya na naira dubu Goma ga masoyanta, Hadiza Gabon ta bayar da wannan kyautane a matsayin goron Juma'a wanda dama a baya ta saba bayarwa amma kwana biyu tadan dakatar, a shekaranjiya wani ya tunamata cewa ta daina basu kyautar katin waya ashe Hadizar taji wannan kira sai gashi kiwa yau ta bayar.Hadizar ta saka katunan waya na dari biyar biyar guda sha biyu da kuma na dubu daya daya guda hudu a dandalinta na shafin Instagram tace gashi masoyanta su saka kyauta kuma tayi kira ga wanda ya samu sai yayi comment.

Allah ya yiwa Hadiza Gabon Hannun kyauta domin ko a sallar data gabata saida ta yanka katon sa guda ta bayar da naman kyauta ga makwabtanta sannan kima ta dafa abinci ta rabawa mutane.

Haka kuma Hadiza Gabon tayi suna wajen baiwa yara 'yan makaranta tallafin kayan karatu.

Muna mata fatan kamar yanda take saka farin ciki a fuskokin mutane Allah ya biyamata bukatunta ya kuma karomana irinta a cikin Al'umma.

No comments:

Post a Comment