Wednesday, 20 September 2017

Hadiza Gabon ta fara finafinan turanci na kudancin kasarnan

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa Hadiza Gabon ta shiga sahun wasu daga cikin abokan aikinta na masana'antar finafinan Hausa irinsu Rahama Sadau, Sani Danja, Yakubu Muhammad Ali Nuhu da suke taka rawa a finafinan kudancin kasarnan, a wannan hoton Hadizarce tare da fitacciyar jarumar finafinan kudu me suna Mercy Aigbe, sun dauki wannan hotonne a gurin daukar wani shirin fim din turanci na kudancin kasarnan me suna "Lagos Fake Life".


Wasu daga cikin jaruman finafinan Hausa da suka tsallaka kudu suna shirin fim sukan rika yin abubuwan da suka sabawa al'adunmu na Hausa da kuma addininmu na Musulunci da sunan sana'a to ko Hadizar itama zata bi sahunsu kokuwa zata kare mutuncinta?

Hardai wasu masoyanta sun fara bayyana ra'ayoyinsu akan wannan batu inda suke cewa tayi kokari dai ta rike mutuncinta da aka santa dashi.

Muna tayata murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment