Tuesday, 12 September 2017

Hoton me tsaron lafiyar Shugaba Buhari cikin zuba daya yasha yabo

Allah sarki wannan hoton wani hadimin/ daya daga cikin masu tsaron lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buharine cikin zufa lokacin da shugaba Buharin yaje kaddamar da katafaren kamfanin sarrafa kaji na Kaduna, yana sanye da rigarnan ta gwat ce ga zafi amma haka baisa yayi sako-sako da aikinshiba, Hoton yaja hankulan mutane a shafukan sada zumunta da muhawar wasu sun rika fadin waishi bashi da hankicine(abin goge zufa?) wasu kuma sunce tsabar tsare aikine kawai yasa haka.Da damadai sun yabawa wannan mutumin inda sukace wannan shine aikin dan kasa na gari.

Kwararren me daukar hotonnan na shugaban kasane Bayo Omoboriowo ya dauki wannan hoton.

No comments:

Post a Comment