Monday, 25 September 2017

"Irin gwagwarmayar da Sani Danja da Adam A. Zango keyi da mutane ko shugaban kasa bazai iyaba">>Mansurah Isah

Lallai ran Mansurah Isah ya baci sosai saboda irin furucin batancin da wasu mutane ke yiwa 'yan fim, Mansurah ta caccaki irin wadannan mutane kuma ta bayyana cewa sufa 'yan fim dinnan mutanene kamar kowa haka kuma a wani batu daya ja hankulan mutane shine inda Mansurar ta bayyana cewa irin gwagwarmayar da Mijinta Sani Musa Danja Zaki da Adam A. Zango suke dauka na mutane ko wani shugaban kasar bazai iya daukaba.Gadai abinda Mansurar tace:

"Yan film din nan da kuke maganar su, suna da iyalai, yan uwa, makota da dangin nesa Dana kusa, Wanda a duk lokacin da matsala ta taso musu in dai yafi karfin su, to wajen dan film zasu kawo, koda baida kudi a lokacin, sai yayi iya kokarin sa ya taimaka. Irin su sani danja, Adam zango da sauran su, case dake hannun su wani shugaban kasan bazai iya dauka ba. Domin kallon kudi ake musu a koda yaushe, kuma Zaa iya samun su ba tareda ansha wahala ba. Kuma haka suke taimakon. Muna kawo wassu case din media ne, badan komai ba, sai dan in akwai mai hali kuma niya sai ya taimaka. Wani case din yafi karfin mutum daya. Akwai dayawa mutan gari ko wayana baa dauka dan ansan maganar taimako ne, wassu ma guduna suke, wassu Wanda na kai musu basu gama ba, balle nace ga wani. Ya kamata ku gane, ba sai Ana muku bayanin rayuwa ba kamar kananan yara, shi yasa ake son kuna ziyartar marasa lafia da marayu da sauran su. Zaku San cewa duniyar gabakin dayanta sai addua."

No comments:

Post a Comment