Monday, 25 September 2017

"Jama'a Ku daina yiwa 'yan fim kudin goro bakusan aikin alherin da sukeyi a boyeba">>Mansurah Isah

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa matar Sani Musa Danja Zaki, Mansurah Isah taja hankulan wasu mutane da suke yiwa jaruman finafinan Hausa kudin goro a duk lokacin da aka samu wata ko wani jarumi da yin ba daidaiba, Mansurah tace suma fa mutanene kuma musulmai kuma masu zagin nasu basusan irin ayyukan alherin da suke aikatawa na farantawa Allah a boyeba.Ta kara da cewa akwai jarumai da dama da take samu akan nemawa wasu bayain Allah da suke cikin halin kaka nikayi taimako kuma haka wadannan jaruman zasu bayar da taimako su kuma bukaceta da kada ta bayyanawa Duniya.

Gadai cikakken bayanin da Mansurah tayi:

"Assalamu alaikum. Yan uwana musulmai, wallahi wallahi kuji tsoron Allah. Ku tuna akwai hisabi, Duk abinda yan film sukayi, sai kunyi suka. Kar ku shiga tsakani BAWA da UBANGIJIN sa, domin bakusan abinda yake yi a boye dan farantawa ubangiji rai ba. Mun kawo case din UMMASALAMA domin a ceto ranta, wacce take bukatan taimako cikin gaggawa, wassu suka fara zagin yan film, wai mai sukeyi, Ina duk kudin da suke tarawa? Ku kusan abinda yan film din sukeyi? Ko halin da suke ciki? Shi yasa duk Sanda wani ko wata yar film ta kirani dan taimakawa, nakan so, na rubuta ba dan komai ba, dan asan abinda sukewa jamaan gari. Akwai case din yara da aka haifa da #diabeties, a nan na rubuta cewa duk wata suna bukatan #insulin domin Karin lafiyan su, waya tuna dasu a watan nan? Babu sai Yan film. Case da muke dashi bana ummasalama kadai bane, muna da case irin na ummasalama sunfi thousands ( dubu ), ko kusan guda nawa yan film suka biya musu kudin asibiti ko magani? Ko aika musu da kayan abinci? Kuma mutanen nan ba yan film bane. @adam_a_zango @officialsanidanja @yakubu_mohd @realalinuhu musha case dasu, duk Sanda na kai musu case din wassu dan su taimaka. Sai nayi musu alkawari cewa banzan fadawa kowa ba ko na rubuta a page Dina. Nasha nuna musu cewa gara duniya tasan abinda kukayi, domin wassu mutane jakuna ne, basu tauna magana kafin su fada, yan film suna iya kokarin su na taimakawa al'ummah Wanda ba yan film ba, Amma da zarran case na yar film ta taso, sai ku fara zagi kamar su ba musulmai bane, kamar in kun taimaka haram ne, kai kayi aikin ladan ka mana, tsakanin ka da ubangijin ka in kana da hali. Ka barwa Allah komai. Nasha kawo case page Dina, wallahi Christians sun sha min dm na bada gudunmowa, har mamaki suke bani, Amma wai musulmi ne zai fara zagi da zarra kace ya taimaka, ko waya kayi musu, zasuyi alkawari bazasu cika ba. Ina mai bada hakuri ga mijina da sauran yanfilm da ake zagi a dalilina, suyi hakuri su kuma ci gaba da aikin lada. Kuma neman taimako ta kowacce iri ne, banzan daina neman wa mutane ba, in har naji labari ko an kawo min case dinsu. Allah ya shige mana gaba ameen. Allah ka bani ikon ci gaba da taba rayuwan al'umman ka domin shine farin cikina."

"Ni tambaya ta a nan, kudin yan film ne kadai ake taimako dashi? Ko kuwa su kadai Allah yace suyi taimako? Ina laifin Wanda yace, wa mai son aikin lada gashi yayi? Ba'ace dole a taimaka ba, duk mai so ko mai hali bisimillah. Kai a matsayin ka na musulmi ai ya kamata kasan cewa duk abinda bawa zaiyi, sai Allah ya yarda mishi, aure, haihuwa, shiriya, arziki, taimako, lafia, mutuwa duk sai da yardan ubangiji. Kar ku bari bakin ciki da jahilci yaci gallaba azuciyan ku. Shikenan in dan film yayi sallah sai yace Allah kayiwa yan film albarka su kadai? Ko Wanda ba dan film ba, sai yace Allah yayiwa mutane albarka Amma banda dan film? Duk daya muke a gaban ubangiji. Wallahi taimakon da yanfilm sukeyiwa a waje, ba kadan bane. Amma baku gani. Daga anyi magana sai kuce dan film. Why? Menene dan film ne? Wata hallita ce daban ko yaya? Ba uwace ta haife su ba ko ba bayin Allah bane? Ko akwai inda aka fada acikin alqurani cewa kayi taimako Amma banda dan film ? Allah ubangiji ya saka da alheri ga dukanni masu taimako, Wanda suke taimakawa a boye dana fili ameen. Allah ya shirye mu gabaki daya. Masu taimako Allah ka Kara musu budi ameen, masu niya kuma Allah kada iko ameen."

Sai muce Allah shi kyauta.

No comments:

Post a Comment