Thursday, 7 September 2017

Jifar shedan ta kare da daukar hoto

Wannan hoton wani bawan Allah mahajjacine daya karade shafukan sada zumunta, mutumin ya dauki kanshi hotone a lokacin da yake jifar Shedan hakan yasa da yawan mutane da sukayi sharhi akan wannan hoto nashi ke nuna cewa lallai wannan mutumi abinda yayi be kyauta ba, domin yana cikin halin bautar Allah ne sannan kuma ya shagala da wasa da wayarshi.



Wasu sun rika cewa "wannan ai shi shedandin ya jefa" wasu kuma da yawa cewa sukayi, cikin barkwanci, ya dauki hotonne dan ya tabbatar da cewa lallaifa ya jefi shedan koda shedandin zaiyi kokarin karyatashi.

No comments:

Post a Comment