Thursday, 21 September 2017

Jihohin Kano da Osun sun bayar da hutun sabuwar shekarar musulunci

Gwamnatin jihar Osun karlashin jagorancin gwamna Rauf Aregbesola ta bayar da hutun kwana daya wato ranar Alhamis domin shigowar sabuwar shekarar addinin musulunci ta 1439 bayan hijirar annabi Muhammad S.A.w.Haka itama gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje  ta bayar da hutun sabuwar shekarar musuluncin ranar Juma'a me kamawa.

Allah ya bamu ikon aikata ayyukan alheri a cikin wannan sabuwar shekara

No comments:

Post a Comment