Saturday, 23 September 2017

Kalli kudin tarar da aka sawa kananan yara da suka aikata laifi

A ziyarar datakai gidan yarin da ake daure yara a jihar Kano, tsohuwar jarumar fim din Hausa, matar Sani Danja Zaki wato Mansurah Isah tare da kawayenta tace taga abin tayar da hankali domin wasu yaran kudaden da ake tsare dasu basu taka kara sun karyaba amma saboda iyayensu basu dashi dole suka barsu a tsare haka kuma tace wasu fadane yakaisu gurin wasu kumama sharri aka musu. Tayi kira ga mutane dasu saka hannu a tallafa a kaiwa wadannan yara dauki domin aikin bana mutum daya bane.Gadai abinda ta rubuta a dandalinta na sada zumunta kamar haka:


"Assalamu alaikum, sunana Mansurah isah. Ina rokon Al'umman musulmai, maza da mata da su taimaka su ceci rayuwan yaran nan da suke inda ake ajiye yara da sukayi laifi, wallahi wallahi wani yaron laifin shi bai taka Kara ya karya ba, wani yaron ma sharri kawai akayi mishi, na rasa yanda zanyi, na rasa wa zan kaiwa kukana. Ina rokon ku da ku dubi yaran nan da idon rahama, ku fiddo su daga gidan nan. Zakuga cewa wassu iyayen basuda kudin da zasu fidda yaron su. Mai zanyi? Ya zanyi ? Naje prison, naje gidan mahaukata, naje gidan da ake ajiye yara da sukayi laifi, wani yaron ma fada ne ya hadasu aka kulle shi. Ku taimaka ku ceci yaran nan, mutum daya bazai iya ba. Dole ne sai mun hada hannu, mun taimake su. Please. Allah ubangiji ya bamu ikon taimakawa ameen. Allah ubangiji ya shirya mana zuria ameen, Allah ubangiji ya raya abinda muka haifa ameen. Na barku lafia."

Muna fatan Allah ya sakamata da alheri.

No comments:

Post a Comment