Saturday, 23 September 2017

Karanta labarin 'Yar siyasa dake kwana uku batayi wankaba


Wacce irin sadaukarwa za ka yi domin alkinta ruwa?

Ita dai shugabar gwamnatin lardi ta Afirka ta kudu na ganin za a iya yin komai domin alkinta ruwa.

Firimiyar Yammacin Cape Helen Zille ta ce tana yin kwana uku ba ta yi wanka ba.
Duk da wasu na ganin hakan kamar bai kamata ba, a zahiri tana da dalilai masu karfi na daukar matakin.Kun san dalilinta na yin wanka sau daya a kwana uku? Yankin Yammacin Cape - wanda ya yi suna wajen tsaunuka da bakin teku - yana fama da matsanancin karancin ruwan sha wanda ya yi kamari saboda farin da yankin ya fada a shekarar da ta wuce.

"Ina yin wanka ne a takaice, kuma sau daya a kwana uku. A sauran kwanakin makon kuwa nakan wanke hannayena ne. A baya nakan wanke gashin kaina a kullum, amma yanzu kwaskwarima kawai nake yi," in ji Ms Zille a wata makala da ta wallafa.

"Sai dai kuma ina ganin gashi mai maiko a matsayin wata alama ta nuna matsayi."
Duk da haka Ms Zille, wacce da ita aka kafa jam'iyyar hamayya ta Democratic Alliance (DA), ta bai wa mutane da dama mamaki da wadannan kalamai nata.

Ms Zille babakuwa ba ce wajen janyo ka-ce-na-ce. A kwanan baya ta janyo ce-ce-ku-ce bayan ta wallafa wani sakon Twitter inda ta ce wani bangare na mulkin-mallaka alheri ne.
'Yan kasar Afirka ta kudu na ganin rashin yin wanka ba wani babban abin damuwa ba ne.
Mazauna yankunan marasa galihu na Cape Town na dogara ne da wani famfo da al'umar ta kafa wajen samun ruwan wanka, yayin da mazauna yankunan da ke samun matsakaicin kudin shiga ke samun ruwa a famfunan giadajensu.

Amma kalaman da shugabar ta yi wata hanya ce ta sake yin nazari kan yadda ake yin amfani da ruwa.

Yanzu me muka sani game da yadda daya daga cikin 'yan siyasar Afirka ta kudu ke kula da kiwon lafiyarta?

A kwanan baya ne aka caccaki Ms Zille a wata makala da aka wallafa a TimesLive inda aka yi tambayoyi kan yadda shugabar lardin ke kashe harajin da ake karba wajen samar da ruwan sha a gidanta na gwamnati da ke Cape Town.

A yayin da take nuna cewa ta dauki matsalar karancin ruwan a matsayin wani babban al'amari, Ms Zille ta ce "Ni da mijina muna yin amfani da ruwa maras yawa ta yadda, a wasu lokutan nakan damu kan yanayin kiwon lafiyarmu."

Wannan labari ka iya sa wa masu amfani da shafukan sada zumunta su sarara, amma ga mutanen da ke yankin da ke fama da karancin ruwa, batun ba na wasa ba ne.

Zurfin ruwan da ake da shi a yankin Yammacin Cape kashi 35 cikin 100‚ wato ya ragu da kashi 61 idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekarar da ta wuce, in ji sashen samar da ruwan sha na lardin.


Yanzu kuma an sanya takunkumi kan yawan ruwan da za a yi amfani da shi a lardin, inda ba za a kyale kowanne mutum ya yi amfani da fiye da lita 87 a kowacce rana.

Za a ci tarar duk mutumin da ya yi amfani da ruwa da yawa, kuma za a dauki tsattsauran mataki kan wuraren kasuwanncin da suka yi amfani da ruwa fiye da kima.

Sai dai da wahala a tilasta wa mutane kan yadda za su yi amfani da ruwa, don haka an fi mayar da hankali waurin rarrashinsu.

Hukumomi sun ce daidaikun jama'a da wuraren kasuwanci ba sa yin biyayya ga wannan doka.

Lardin na dubawa yiwuwar bullo da wata hanyar ta samun ruwan sha, ciki har da sake yin amfani da ruwan da aka gama aiki da shi da kuma hako ruwan da ke karkashin kasa.
bbchausa

No comments:

Post a Comment