Tuesday, 12 September 2017

Kuma dai: Takalmin Amaryar dan Yariman Bakura Khadija Danlami Alhassan ya ja hankulan mutane saboda dankaren tsadarshi

A cikin shagulgulan bikin su da aka fara, dan tsohon gwamanan jihar Zamfara Sanata Sani Yariman Bakura wato Abba da Amaryarshi Khadija sunyi wani taron in abincin dare inda akayi wata gasar daga takalmin juna tsakanin amarya da ango, ananne kuwa hankulan mutane suka karkata kan takalmin amaryar domin yana da dankaren tsada, takalmin nata dai ana sayar dashi akan kudi dalar Amurka dubu biyu da dari da hamsin wanda idan aka kwatanta da kudin Njeriya sun kai sama da naira dubu dari bakwai da tamanin.
Wannan yasa mutane suka rika bude baki cikin mamaki da fadin lallai wannan amaryar yar gatace. muna musu fatan alheri da kuma Allah ya sanya albarka a wannan aure nasu.

Shahararren me daukar hoto Maigaskiyane ya dauki hotunan a wajen bikin da aka gudanar a garin Abuja, idan Allah ya kaimu ranar juma'ane za'a daura auren.

No comments:

Post a Comment