Wednesday, 27 September 2017

"Kwanannan zanyi Aure">>Rahama Sadau


Fitacciyar jarumar finafinan Hausa da aka kora ta koma taka rawar gani a finafinan yankin kudu wadda da yawa musamman daga yankin Arewa ake mata kallon  'yar Duniya saboda irin shigar da takeyi da kuma wasu abubuwa da takeyi a finafinan turanci wanda suka sabawa al'adar mutanen Arewa da kuma addininta na musulunci wato Rahama Sadau tace kwanannanfa zata zama amarya itama ta shige dakin mijinta ta huta da surutan da mutane keta mata nan da can, mutane da dama zasuji mamakin wannan labarin domin da yawa a ganinsu bata cikin jaruman da akewa kallon yin aure nan kusa kai wasuma suna da tunanin cewa wanene zai fito ya auri irin wannan budurwa haka da ake ganin idonta ya bude da yawa?.Rahama Sadau ta bayyana hakane a dandalinta na shafin Twitter yayin da take mayar da martani akan wata magana da wani abokin aikinta jarumin finafinan kudu Timi yayi a dandalinshi na shafin Twitter inda ya saka kaya masu kyau ya kuma rubuta cewa "gayyatarni zuwa gurin aurenka/ki. Ita kuma Rahama Sadau ta mayar da martanin cewa "(zan gayyaceka aurena)kwanannan /bada dadewaba".

Lokaci dai zai bayyana mana yanda zata kasance.

No comments:

Post a Comment