Thursday, 28 September 2017

"Da muji kunya gara muji yunwa">>Nazir Ahmad da Amaryarshi

Shahararren mawakin Hausa Nazir Ahmad Sarkin Waka tare da Amaryarshi Halima kenan a wannan hoton nasu da yayi kyau, muna musu fatan alheri kuma Allah ya kara dankon soyayya.


A gaskiya Nazir Ahmad ya cancanci yabo lura da irin wadannan hotunan daya dauka da matarshi, a irin wannan zamani da ake daukar hotuna da 'yan mata na kamin biki wadanda bama a daura aureba kaga saurayi suna ta rungume-rungume wai da sunan hoto, amma kalli Nazir duk da matarshice ko hannunta be kamaba gaskiya wannan abun sha'awane kuma hakan ya nuna yana kokarin kare koyarwar addininshi, al'adarshi da kuma mutuncin kanshi, idan masu bibiyar shafinnan na hutudole.com basu mantaba haka koda a hotunansu na kamin biki da muka wallafa ko hada jiki basu yiba. Dan zakayi abu daidai da zamani bawai sai ka sabawa Allah ba.

Muna mishi fatan alheri.

No comments:

Post a Comment