Monday, 11 September 2017

Lokuta daban-daban da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya durkusa dan gaishe da Sarakuna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai yayi suna wajen nuna rashin girman kai da durkusawa a duk lokacin dazai gaishe da iyayen kasa masu rike da sarautar gargajiya duk da cewa yana a matsayin zababben gwamna. Hausawa na cewa durkusawa wada ba gajiyawa bane kuma shi hali zanen dutsene idan mutum ya saba da abu da wuya kamin ya canja, musamman idan abunnan me kyaune.A jiyane Gwamna Nasiri El-Rufai yajewa basaraken garin Legas ziyara kuma acan ma saida ya duka kamin ya gaishe dashi, wannan yasa shafin hutudole.com ya tattaro muku hotunan lokuta daban-daban da Gwamna Malam Nasiru ya dukawa sarakunan gargajiya.

No comments:

Post a Comment