Thursday, 28 September 2017

Mahaifi ya kusa burmawa danshi wuka bayan da yaci bashi ya tura dan nashi cirani kasar Finland amma dan nashi ya dawo bayan sati uku wai sanyi yayi yawa acan

Wannan wani labarine me ban takaici ban tausai da kuma ban dariya duk a lokaci daya.

Wani bawan Allahne me suna Peter ya kammala karatunshi na jami'a kusan shekaru bakwai da suka gabata amma bai samu aikin yi ba, sai yaji labarin wani abokinshi dake kasar Finland ya kirashi a waya yake cemai yazo ci rani su nemi arziki tare, nan kuwa Peter ya baiwa babanshi labari, babanshi yana da rufin asiri amma ba me kudi bane, haka dai akayi cika-cikaro tsakanin 'yan uwa hadda bashi aka hadawa Peter kudin tafiya kasar Finland. Sati uku bayan tafiyarshi sai gashi ya dawo gida, mahaifiyarshi na ganinshi ta fashe da kuka tayi tunabin wani abune ya faru.Peter ya zauna ya fara bata labarin shifa sanyi yayi yawa a kasar Finland shiyasa gaskiya yaga bazai iya zama ba ya dawo gida abinshi, cikin takaici hawayen dake zuba daga idanunta suka kafe ta tashi ta bashi guri, haka shima babanshi da ya ji labari ya zauna cikin takaici washe gari ko gurin aiki be iya fitaba saboda bakincikin Peter.

Shikuwa gogan naku yana can ya fita cikin unguwa da yake dama sanannene yaci gaba da sha'aninshi cikin abokai. Da dare yayi ya dawo gida yaci abinci ya kwanta akan kujerar dake falo yayi bacci.

Can tsakiyar dare babanshi ya taso ya ganshi yana bacci a falo, ya tsaya yana kallonshi cikin takaici sai zuciya ta rayamai mugun abu, ya tafi ya dakko wuka yazo kan Peter ya tsaya yana tunanin ya burmamai kawai ya kasheshi ya huta, wata zuciyar tana gayamai kada yayi.

Yana cikin wannan yanayine sai kanin Peter da shima yake kwance a falon, ya daga kai yaga babansu da wuka sai ya kurma ihu, dama ba bacci yake ba yana latselatsen wayane da yaji baban nashi yana fitowa sai yayi likimo, nan baban ya yadda wukar ya fadi kasa yana kuka mahaifiyar Peter itama ta fito data fahimci abinda ke faruwa itama ta dora hannu aka taita kuka a wannan daren basu sake yin bacciba.

Wai idan kaine wane irin mataki zaka dauka akan Peter?

No comments:

Post a Comment