Friday, 8 September 2017

MAINENE TA'ADDANCI ?>>Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Image may contain: 1 person, eyeglasses and closeup
TAADDANCI SHINE : DUK WANI YINKURI NA ZUBAR DA JINI, KO KISAN KAI, KO CIN MUTUMCI,GA WANI BA TARE DA HAKKI BA , WANDA SHARIA TA AMINCE. 

ANAYIN TAADDANCI DA SUNAYE IRI IRI, DA MANUFOFI , WANDA 'YAN TAADDA SUKE FAKEWA DA SU. KAMAR BAMBAMCIN ADDINI, KO KABILANCI, KO YARE KO SIYASA.

MASALIN : TAADDANCI, AKAN DUKIYA, SATA, FASHI, DA MAKAMI, KWACE, GARKUWA DA MUTANE, 

MASALIN TAADDANCI AKAN RAYUWA, KISAN KAI, MUTUM YA KASHE KANSA, SABIDA WATA DAMUWA, KO WANI YA KASHE SHI, KO SHI YA KASHE WANI, YAN BINDIGA DADI, DA DUK WANI MAI KASHE MUTANE, DON SON RAI.

CIN FUSKA, CIN MUTUNCI, BATA SUNA, BAKAR MAGANA, SHAGUBAI, ZUNDAI, DA MAKAMANTANSU. 

MANZON ALLAH (S.A.W) YACE, DUKKAN MUSULMI, AKAN MUSULMI, HARAMUN NE, JININSA DA DUKIYAR SA DA MUTUNCINSA.

No comments:

Post a Comment