Saturday, 23 September 2017

Majalisar dinkin Duniya zata taimakawa musulmin Rohingya bayan ankarar da shuwagabannin Duniya da shugaba Buhari yayi akansu

Image may contain: 1 person
Jaridar Vanguard ta buga labarin cewa majalisar dinkin Duniya tayi kintacen za'a kashe zunzurutun kudi har dalar amurka miliyan dari biyu dan tallafawa musulmai 'yan kabilar Rohingya su sama da dubu dari hudu dake gudun hijira a kasar Bangladesh dalilin kisan rashin imani da kare dangi da ake musu a kasar Myanmar ko kuma Burma, Majalisar tayi wannan hobbasane bayan da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi kiran da a tallafawa musulmin Rohingyan a jawabin da yayi a taron majalisar dinkin Duniya da aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka.


Lallai shugaba Buhari yayi abin yabo kuma ya tabbata gwarzon namiji, haka kuma wannan abin bajinta da yayi zai karo mai masoya a ciki da wajen kasar Najeriya, muna fatan Allah ya karo mana irinshi ya kuma kramai kwarin gwiwa. Amin.

No comments:

Post a Comment