Monday, 11 September 2017

Mamman Daura ya kira matar shugaban kasa H. Aisha Buhari da sunan "yar kunar bakin wake daga Yola"

Anjiyo wata hirar wayar hannu tsakanin dan uwan shugaban kasa Mamman Daura da wani abokinshi Mamman Tukur lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yke kasar Ingila yana jiyya, a cikin hirar tasu sun tattauna batun rashin lafiyar shugaban kasa da kuma irin yanda yake samun sauki haka kuma sun ambaci matar shugaban kasar inda suka kirata da sunan "yar kunar bakin wake daga Yola".


Hirar tasu ta tabo batun tsohon shugaban hukumar kula da leken asiri ta kasa da aka kora dalilin wasu makudan kudi da aka gano jibge a wani gida dake da alaka dashi wato Ambasada Olusola Oke, kamar yanda Mamman Daura ya fadi a cikin hirar wayar Olusola ya baiwa mutane cin hanci ciki harda shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki akan su goyi bayanshi.

Shafinnan na tonon silili wato Sahara Reporters ne yayi ikirarin samun wannan hirar waya.

No comments:

Post a Comment