Tuesday, 12 September 2017

Masu bautar kwarya a kasar China

Kabilar Lahu na daya daga cikin kabilu 56 na kasar Sin. ‘Yan kabilar suna bauta wa kwarya a matsayin gunkinsu, saboda a tatsuniyarsu, a da can, akwai wani namiji da mace ‘yan kabilar Lahu da suka tsira daga ambaliya saboda boya da suka cikin wata babbar kwarya. Bikin kwarya shi ne biki mafi kasaita ga ‘yan kabilar, inda a kan sanya wani katuwar kwarya a babban fili a kuma shafe kwanaki uku a kowace rana ana rawa da waka da sauran shagulgula.

Allah mun godemaka ka kara shiryar damu hanya madaidaiciya.
Daga Cri Hausa

No comments:

Post a Comment