Sunday, 24 September 2017

Mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya Amina Muhammad abin alfaharin Arewa da Najeriya

Mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya Amina Muhammad ta kasance wata abin kallo da son yin koyi ga matan Arewa kai harma da Najeriya baki daya, anan dubun dubatar mutanene suka taru a yayin da ake kaddamar da wani shiri na majalisar dinkin Duniya dazai kula da inganta rayuwar al'ummar Duniya me suna SDGs a takaice, Aminace nan takewa jama'a jawabi a gurin taron.Wani abin birgewa da Amina shine har yanzu baata canja shigartaba, atamfa irin wadda matan Najeriya ke daurawa da zani ko siket da gyale da dankwali har yanzu take sakawa.

Muna mata fatan alheri da kuma Allah ya kareta ya kuma kara daukakata.No comments:

Post a Comment