Friday, 15 September 2017

Matar shugaban kasa Hajiya A'isha Buhari ta amshi bakincin matar shugaban kasar Uganda Janet Kataaha Museveni

Uwargidan shugaban kasa Hajiya A'isha Buhari ta karbi bakuncin uwargidan shugaban kasar Uganda Janet Kataaha Museveni data kawo ziyara a Najeriya ayau,  iyayen kasar sun tattauna akam batutuwan cigaba da taimakon juna.


Janet wadda kuma ministar ilimi da wasanni ce a kasarta tace tazo Najeriyane domin taji kuma ta koya daga irin yanda matar shugaban kasa H. A'isha Buhari take tallafawa mata da kananan yara wajan cigaban rayuwarsu.

Matar shugaban kasa H. A'isha Buhari ta bayyanawa Janet irin yanda ta bude gidauniyar Future Assured wadda take amfani da ita wajen tallafawa mata da kananan yara da kuma matasa wajen inganta rayuwarsu ta fannonin Ilimi kiwon lafiya dadai sauransu.
No comments:

Post a Comment