Monday, 25 September 2017

"Musulmai kadai zan yiwa wanki da guga">>inji wani me sana'ar wanki da guga

The signboard placed at the entrance to the launderette. - Picture from Facebook
Wani mutum me sana'ar wanki da guga a garin Muar dake jihar Johor ta kasar Malasiya ya saka alamar sanarwa a kofar shagonshi dake cewa musulmai kadai yakewa wanki da guga, wannan sanarwa da ya saka ta jawo cece-ku-ce tsakanin wasu mutane yanda 'yan jarida suka tururuwa zuwa shagonshi danjin dalilinshi na wannan sanarwar daya fitar.Saidai wani malamin kasar na malasiya da yayi sharhi kan wannan batu yace ba laifibane domin wannan mutumin ya fadi haka saboda a addinin musulunci da kuma kowace irin sana'a ana bukatar tsafta saboda haka shi wannan me sana'ar wanki beyi laifiba amma be kamata a rika watsa maganarba saboda kada wadanda ba musulmaiba su yiwa abin mummunar fahimta.


No comments:

Post a Comment