Tuesday, 26 September 2017

Nafisa Abdullahi 'yar kwalisa, wadannan hotunan nata sun jawo cece-kuce

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa Nafisa Abdullahi kenan cikin matsattsiyar riga data nuna siffar jikinta da yawa, kai ba dankwali, rike da kugu, in banda rashin dankwali da mayafi hoton yayi kyau.


Dayawa dai da sukayi sharhi akan wadannan hotunan na Nafisa sunce basu dace ba a matsayinta na musulma ta rika nunawa duniya surar jikintaba, haka kuma wasu suncemata karta biyewa Rahama Sadau ya kamata ta zama me kamun kai.Karanta abinda mutane ke cewa akan wadannan hotunan na Nafisa.

No comments:

Post a Comment