Wednesday, 27 September 2017

Namu yayi abin yabo: Salihu Dasuki ya zama babban malamin jami'a mafi karancin shekaru a wata jami'ar kasar Ingila Abin alfaharin Arewa da Najeriya

Wani haziki dan Najeriya daga yankin Arewa me suna Dr Salihu Dasuki ya zama malamin jami'a mafi karancin shekaru a jami'ar Sheffield Hallam dake kasar Ingila, Salihu dan shekaru 29 yayi digiri da digirgir a fannin kimiyyar labarai wannan yasa Jami'ar ta ingila ta sakashi cikin  manyan malamanta da fara aikinshi.

Yana dan shekaru ashirin da daya ya gama digirinshi na farko Salihu ya samu sakamako me daraja ta daya wanda ake kira da (First Class) a turance ta fannin kimiyyar sadarwa daga jami'ar Eastern Mediterranean dake kasar North Cyprus, daga nan Salihu ya tafi Jami'ar Brunel ta kasar Ingila inda yayi digirinshi na biyu shima a fannin kimiyyar sadarwa ya kuma cigaba ya samu digirin digirgir na dacta a shekarar 2012. A wancan lokacin shine mutum mafi karancin shekaru dake da digirin Dacta a yankin Arewa kaff.
   
Tun bayan daya samu wannan aiki yake ta samun sakonnin taya murna daga mutane daban-daban a ciki da wajen kasarnan, hatta me magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu saida ya tayashi murna.
Haka kuma saboda kyawun takardunshi na makaranta Salihu ya shiga cikin mutane guda dari da ake ji dasu a yankin Arewa a shekarar data gabata ta 2016.

Haka kuma shekaru biyar da suka gabata lokacin Salihu yana Najeriya kuma yana da shekaru ashirin da hudu kacal ya kasance mataimakin farfesa kuma yayi koyarwa a fitacciyar jami'arnan ta kasar Amurka mallakin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar dake jihar Adamawa.

Muna tayashi murna da fatan Allah ya kara daukaka kuma yasa wannan ya zama karin karfin gwaiwa ga dalibai masu tasowa.

No comments:

Post a Comment