Saturday, 23 September 2017

Rahama Sadau ta zama fitacciyar/mafi shahara a finafinan turanci na kudancin kasarnan

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa da aka kora ta koma yin finafinan turanci na kudancin kasarnan Rahama Sadau ta kara samun wata gagarumar cigaba a harkar shirin fim din kudu da takeyi, Rahama ta shiga cikin wadanda zasu lashe gasar  fitattun jaruman finafinan turanci na kudu wadda ake kira da BON a takaice.Tundai bayan korarta da akayi daga finafinan Hausa likafarta taketa cigaba take kuma kara samun hawa matsayi kala-kala a harkar finafinai.
A cikin wata hira da Rahama tayi kwanaki da jaridar ThisdayStyle tace duk abinda zatayi takanyi kokari ta kare mutuncin addininta da kuma yankin da ta fito daga ciki.

To saidai a addinin Musulunci babu tsarin mace ta fitar da gashin kanta waje kamar yanda rahamar tayi a cikin wadannan hotunan.
Muna tayat murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment