Saturday, 9 September 2017

"Sau biyu tana zuwa dakina bayan tayi aure"

Image result for photo of man and woman holding hands
Lallai akwai mutane masu kalar halayya daban-daban wanda su basu dauki sabon Allah komi ba ya zamar musu jiki, dukkaninmu masu sabone, amma mutum ya aikata aikin sabo a boye yazo kuma yana gayawa jama'a wannan kuma wani abune da daban. Wani bawan Allah yayi wata magana a kusa dani da abin ya bani mamaki na dade yana min yawo a zuciya.

Naje kasuwa siyan wani abu, me shagon beda abinda nazo siya sai ya tafi ya nemomin, muna zaune tare da wani mutum sai ga wani abokinshi ya shigo yana danna waya yake nuna mishi wata budurwa suka fashe da dariya, sai dayan yake tambayarshi "kai wai ina wance dana taba gani a layinku?" sai yake cemai ai tayi aure 'ya 'yanta biyuma yanzu.


Ya kara da cewa "kasan da aurenta zuwan ta biyu dakina?" sai suka kara fashewa da dariya.

Wannan magana da yayi tasa hankalina ya dawo gurinsu sosai har saida na waiga na kalleshi, hakan yasa yayi kasa-kasa da muryarshi, lallai wannan abu ya munana, matar aure koda kinyi abubuwan da basu kamata ba kina budurwa ai darajar aure da amanar mijinki dake kanki ya isa ace kinji tsoron Allah kin daina, bawai macen bace kadai ke da laifi, amma a irin wannan yanayi gaskiya duk abinda ya faru itace keda kaso mafi tsoka saboda tana da aure.

Me macen aure zataje yi dakin tsohon saurayin ta?

Bata da wata hujja kuma kaima wataran zakayi auren in baka dashi, ya zakaji idan ka hadu da mata irin wannan?, karfa mu manta kamar yanda kayi haka za'ayima.

Haka shima labarin wani bawan Allah daya rage saura sati biyu daurin aurenshi ya gamu da budurwar tashi dazai aura akin wani saurayinta, daga nan yace dama  yanata rokon Allah idan alherine Allah ya tabbatar idan kuma ba alheribane Allah canjamai da mafi alheri.

Irin wannan abu na zuwwa dakin saurayi da wasu 'yan mata keyi gaf da zasuyi aure har suna aka samishi wai "die minute". Yakamata dai da samari da 'yan matan su gane su tuba, domin duk abinda kayi sai an maka, Allah ya rabamu da 'yan die minute suma masu yi Allah ya shiryesu.


No comments:

Post a Comment