Wednesday, 27 September 2017

Saudiyya ta ba mata damar tuka mota

Wata Mata
Hukumomin kasar Saudiyya sun bai wa matan kasar damar fara tuka mota, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana.
Matakin ya biyo bayan wata sabuwar doka ce da Sarki Salman ya yi wadda ta amince a bai wa matan lasisin tuki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya ruwaito.


Kungiyoyin kare 'yan cin dan Adam sun shafe shekaru suna kiraye-kirayen ba mata damar tuki da kansu a kasar.
Kuma hukumomi sun sha tsare matan da suka karya dokar haramcin tukin mota.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment