Sunday, 17 September 2017

Shugaba Buhari ya tafi kasar Amurka dan halartar taron Majalisar dinkin Duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Amurka a yau lahadi, bayan yin taro da gwamnonin jihohin Kano da Borno da Sakkwato, Shugaba Buhari zai halarci taron majalissar dinkin Duniya da za'a gudanar kuma ana saran shugaban zaiyi jawabi a gurin taron.Haka kuma kamar yanda me magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya sanar Shugaba Buhari zai biya ta kasar Ingila idan yana dawowa daga gurin taron, saidai bai bayyana abinda zaiyi a ingilarba.
Muna fatan Allah ya kaishi ya kuma dawo dashi gida lafiya.

No comments:

Post a Comment