Thursday, 21 September 2017

Shugaba Buhari yasha yabo a taron majalisar dinkin Duniya daya halarta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yasha yabo sannan kuma yaba mutane mamaki saboda irin shigar da yayi zuwa taron majalisar dinkin Duniya, bai dauki yan rakiya masu yawaba kamar yanda sauran shuwagabannin baya suka saba yiba da kuma wasu shuwagabannin kasashen Afrika.Motoci hudune kacal suke a cikin tafiyar shugaba Buharida suke kaishi daga masaukinshi zuwa inda za'a gudanar da taron,, shuwagabannin bayadai sun saba zuwa da tawagar motoci kusan talatin da kuma 'yan takiya da yawa, hakan yasa wasu masu sharhi akan lamurran dake wakana a Majalisar dinkin Duniya cikin mamaki har suke tunanin shin wai ko har yanzu Najeriya tana cikin matsin tattalin arzikine?

Sun gane cewa zancen ba haka yake ba da suka kara lura da wasu abubuwan dake tattare da wannan adalin shugaba da babu rayuwar facaka a cikin tsarinshi, hatta irin kayan da shugaba Buhari ya saka a taron majalisar dinkin Duniya na shekarar data gabata da kuma na wannan shekarar kusan dayane babu wani banbanci sosai.

Haka kuma shugaba Buhari na daya daga cikin shuwagabannin da suka isa gurin kamin lokaci saboda  tsare lokaci, jawabin da shugaba jawabin da shugaba Buhari yayi a gurin taron shima yasha yabo daga ciki da wajen kasarnan.

Allah ya karawa baba Buhari lafiya ya kuma shigemai gaba.

No comments:

Post a Comment