Friday, 29 September 2017

Shugaba M. Buhari ya halarci sallar Juma'a inda aka yiwa Najeriya addu'o'i

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci sallar Juma'a ta musamman da akayi a yau inda aka yiwa Najeriya addu'o'i bisa cika shekaru hamsin da bakwai da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka, wannan hoton na shugaba Buhari yana gyara gilashi ya matukar burge mutane kuma an yita watsashi a shafukan sada zumunta da muhawara na yanar gizo.Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da manyan jami'an gwamnati da suka hada da ministoci sun halarci wannan sallar Juma'a tare da shugaba Buhari, muna fatan Allah ya karawa Najeriya zaman lafiya hadin kai da arziki da kuma shuwagabanni na gari.

No comments:

Post a Comment