Monday, 18 September 2017

Shugaba M. Buhari ya isa kasar Amurka gurin taron majalisar dinkin Duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Amurka da safiyar yau litinin inda zai halarci taron majalisar dinkin Duniya da za'ayi, a jiya Lahadine shugaba Buhari ya tafi kasar ta Amurka inda daga can kuma zai biya kasar Ingila.Akwai dai wasu rahotanni dake nuna cewa wasu 'yan fafutukar kafa kasar Biyafara sun shirya wani gangami da zasuyi a kofar ginin majalisar dinkin Duniyar dan kunyata shugaba Buhari, zamu jira mu gani ko shirin nasu zai samu nasara?.

No comments:

Post a Comment