Tuesday, 12 September 2017

Shugaban kasa M. Buhari ya bude katafaren kamfanin sarrafa kaji da abincinsu a jihar Kaduna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kaduna inda ya bude katafren kamfanin sarrafa kayan noma da suka hada da kaji da kwai da abincinsu da sauransu me suna Olam, kamfanin daya shanye zunzurutun kudi dalar Amurka miliyan dari da hamsin zai samarwa da 'yan Najeriya kimanin mutum dubu takwas aiki hadi da kuma likitocin dabbobi guda dari biyu.


Bude wannan kamfani kokarine na Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-Rufai wajan jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje zuwan cikin jihar.


Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amshi ziyarar Shugaban kasar Ghana ayau amma ya fakatar dashi har saida yazo ya kaddamar da wannan katafren kamfani saboda muhimmancinshi da kuma alkawarin zuwa da yayi.

Gwamnan jihar kaduna ya godewa Shugaba Buhari bisa wannan namijin kokari.
Allah ya kara ciyar da Najeriya gaba.No comments:

Post a Comment