Tuesday, 19 September 2017

Shugaban kasa M. Buhari yana sauraren ba'asi daga 'yan rakiyarshi kasar Amurka kamin fara taron majalisar dinkin Duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari kenan a kasar Amurka inda yaje halartar taron majalisar dinkin Duniya inda kasashen Duniya zasu hadu su tattauna batutuwan da suka shafi al'ummarsu, anan shugaba Buhari yana karbar bayanaine daga wadanda suka mai rakiya kamin wayewar gari lokacin da za'a fara taron.Wani abu daya dauki hankulan mutane a wannan zaman jin ba'asi tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da abokan rakiyarshi shine shan hannun da akayi tsakanin me baiwa shugaban kasar shawara akan kafafen sada zumunta na zamani Lauretta Onochie da gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, wasu dai sunce be kamata gwamnan ya gaisa da itaba kasancewar ya fito daga jihar data fara yunkurin kafa shari'ar Musulunci a Najeriya.No comments:

Post a Comment