Tuesday, 19 September 2017

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi a gaban taron majalisar dinkin Duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shuwagabannin Duniya da suka hadu gurin taron majalisar dinkin Duniya karo na 72, shugaban ya taya sabon sakataren majalisar Antonio Guterres bisa mukamin daya samu haka kuma ya yabawa tsohon sakataren majalisar Banki Moon bisa irin gudumuwar daya bayar.

Shugaba Buhari ya kuma yabawa kasashen Italiya da Jamus da sauransu bisa amsar 'yan gudun hijirar kasashen Siriya da Afganistan da Iraki da sukayi.

Haka kuma ya tabo batun Najeriya inda yace Najeriya zataci gaba da bayar da gudummuwa wajen ganin dorewar mulkin dimokradiyya, kuma tana tallafawa 'yan gudun hijira da suka rasa muhallinsu dalilin rikicin Boko Haram da kayan agaji daban-daban. Haka kuma tana bayar da gagarumar gudummuwa a fadan da kasashen da tafkin Chadi ya ratsa ta cikinsu sukeyi da 'yan tada kayar bayan Boko Haram.

Shugaba Buhari ya tabo batun yaki da cin hanci da rashawa inda ya bayyana muhimmncinshi ga cigaban kasa, haka kuma ya bukaci da ayi sulhu da shugaban kasar Korea ta Arewa bisa barazanar makaman kare dangi da takewa kasashe a yayinda shi kuma shugaban kasar Amurka Donald Trump yasha alwashin yin rugu-rugu da kasar.
Muna fatan Allah ya dawo mana da shugaba Buhari lafiya.

No comments:

Post a Comment