Tuesday, 5 September 2017

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya kawo wa shugaba Buhari ziyara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amshi bakuncin shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou a garin Daura yau talata inda shugaban Nijar din ya samu rakiyar gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da kuma sarkin Daura Umar Faruk Umar.FARFADWAR TATTALIN ARZIKIN NAJERIA.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi magana da manema labarai akan labarin farfadowar tattalin arzikin Najeriya da wani rahoto da hukumar kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, NBS, ta fitar daya nuna cewa kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta fada, shugaban yace yaji dadin samun wannan labari amma bazai yi kasa a gwiwa ba har sai yaga cewa talakan Najeriya ya gani a kasa dangane da farfadowar tattalin arzikin.
Shima shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya bayyana cewa ya kawo wa sugaba Buhari ziyarane domin su tattauna batutuwan da suka shafi kasashen nasu guda biyu da suka hada da matsalar mayakan Boko Haram da kuma batun tafkin Chadi dadai sauran batutuwa.


No comments:

Post a Comment