Sunday, 24 September 2017

Subhanallah!: Tayi ridda watanni biyu bayan musuluntarta

Kerala Woman Who Left Home And Converted To Islam Returns To Hinduism
Me karatu ka tuna da hoton wannan baiwar Allah? watanni biyu da suka gabata shafin nan na hutudole.com ya kawo labarin yanda ta musulunta,sunanta Athira amma bayan ta musulunta ta canja suna zuwa A'isha, 'yar kasar Indiyce kuma ita da iyayenta mabiya addinin Hindune amma ita sai tabar gida da zummar zataje ta koyi addinin musulunci a karshedai ta musulunta har sukayi shari'a da iyayenta ta tabbatar da cewa ta musulunta da kyar iyayen suka yadda suka tafi da ita gida a matsayin musulma, domin karanta cikakken labarin danna nan. To yanzu dai ta koma ruwa, domin tayi ridda ta koma addinin Hindu, bayan da wata 'yar fafutukar addinin ta dauketa tatafi da ita tayi mata hudubar shedan na tsawon kwanaki.


Bayan da aka gama shari'a Athira 'yar shekaru ashirin da biyu suka tafi gida ita da iyayenta sai wata me fafutikar kare addinin Hindu ta kaiwa iyayen Athira ziyara har gida ta bukaci da a bata ita suje tadan mata wata huduba ta musamman, iyayen suka amince.

Ai kuwa watanni biyu kenan sai ga Athira ta juyawa addinin musulunci baya ta koma addininta na Hindu, da take yiwa manema labarai karin bayani Athira tace dama bokantane da wa'azin mashahurin malaminnan Zakir Naik suka karfafa mata gwiwar shiga addinin musuluncin.

Kafar watsa labaran Outlookindia data wallafa labarin tace ana tsananta bincike akan sabbin shiga musulunci a kasar domin irinsu na saurin fadawa cikin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addini.

Allah shi kyauta.

No comments:

Post a Comment