Thursday, 21 September 2017

Sunan Muhammad ya samu matsayi a BirtaniyaWani rahoto da hukumar kididdiga ta Birtaniya ta fitar ya nuna cewa sunan Muhammad ya samu gagarumar karbuwa a Ingila, inda ya kasance cikin sunaye 10 da iyaye suka fi sanya wa 'ya'yansu a yanzu.

Sunan na Muhammad wanda kafin wannan lokaci ba ya cikin goman farko da suka fi farin jini, a yanzu ya kawar da sunan William ya hau gurbi na goma a jerin sunayen da aka fi rada wa yara.A alkaluman da hukumar ta fitar ta ce sunan Oliver wanda shi ne na daya cikin sunayen da iyaye ke sanya wa 'ya'yansu maza, ya ci gaba da rike wannan matsayi nasa a yawancin sassan Ingila da yankin Wales, in banda yankin Arewa maso yammaci inda sunan Harry har yanzu shi ne na daya, da kuma Landan da yankunan tsakiyar yammaci inda nan kuma Muhammad ne ya fi farin jini.

bbchausa

No comments:

Post a Comment