Sunday, 10 September 2017

Ta kacame tsakanin wasu masoyan Ali Nuhu da na Rahama Sadau anata zage-zage

Jarumar fim din Hausa da aka dakatar, Rahama Sadau tasha zagi da batanci kala-kala a gurin wasu 'yan gani kashenin masoyan Babban Jarumin Finafinan Hausa Ali Nuhu(Sarki), hakan ya farune dalilin zargin wani kalamin batanci da akewa Rahamar cewa ta fada akan Ali Nuhun saboda wai ba'a sakata cikin jaruman da zasu fito a cikin wani sabon shirin fim din da Ali Nuhun yake shiryawaba me suna Abota.

 Rahotanni sunce an saka Nafisa Abdullahi cikin wadanda zasu fito a cikin shirin na Abota wadda akewa kallon cewa basu shiri ita da Rahamar.

Har ya zuwa yanzu dai Ali Nuhu ko Rahama babu wanda yace uffan, musamman a shafukansu na sada zumunta akan wannan batu, amma wasu masoyansu sai musayar kalamai da zage-zage suke tsakaninsu.

Rahamar dai wadda Ali Nuhu ne ya fito da ita fagen finafinan Hausa har takai ga inda take a yau wasu na ganin cewa idan wannan batu ya zama gaskiya to ta zama butulu domin ta juyawa uban gidanta baya kenan.

Ga kadan daga cikin irin abubuwan da wasu masoyan Ali Nuhun ke cewa akan Rahama Sadau din.
No comments:

Post a Comment