Friday, 15 September 2017

TALAUCIN ILMI: MANZON ALLAH S.A.W YA BAYYANA CEWA KARANCIN ILMI YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA.

 Image may contain: 1 person, eyeglasses and closeup

MASANA SUNA TA MAGANA AKAN TALAUCI DA KARYEWAR TATALIN ARZIKI,

AMMA BAA FIYE MAGANA AKAN TALAUCIN ILMI DA KARANCIN MASANA, A CIKIN ALUMMA, BA .
MALAMAI SUNA MUTUWA, FATARA DA YINWAR ILMI YAYI YAWA A CIKIN ALUMMA.
MANZON ALLAH S.A.W YA BAYYANA CEWA KARANCIN ILMI YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA.
WANI MALAMI YACE: ABUBUWA HUDU SUNA TAFIYAR DA MARTABAR MUSULUNCI


NA DAYA IDAN MUTANE BASAYIN KARATU
NA BIYU IDAN MASUN KARATUN BASA AIKI DA SHI.
NA UKU IDAN MASU AIKI DA JAHILCI SUKAYI YAWA.
NA HUDU IDAN MARTABAR MALAMAI TA FADI A CIKIN ALUMMA.
ALLAH YA BAMU ILMI MAI AMFANI, YA BAMU IKON AIKI DA SHI.

Mallam Aminu Ibrahim Daurawa.

No comments:

Post a Comment