Wednesday, 20 September 2017

Toh fa: Karanta tambayar da bbc basu da amsarta

Fitacciyar kafar watsa labarai ta Duniya bbchausa ta bayar da damar ayi tambaya ta dandalinta na sada zumunta da muhawara inda tace zatayi kokarin ganowa masu tambayar amsoshin tambayarsu, nan take kuwa wani bawan Allah me suna Jabir yayi tambayarshi kamar yanda ake iya gani a hotonnan.Jabir yace "Yauwa bbc tambayata itace menene yasa idan aka kai hari na ta'addanci idan musulmine ake zargi da kai harin sai kuce ta'addancine idan kuma ba musulmi bane sai kuce 'yan bindiga ko wani suna wanda baya daukan ma'anar ta'addanci. Shin ta'addanci aikin musulmai ne kawai ko kuwa riga ce da kowa zai iya sakawa kuma ya cire a lokacin da ya so??? Nasan bazaku dauki tambayata ba saboda bakuda amsarta".

Bayan da Jabir yayi wannan tambaya sai ta zama itace tafi kowace tambaya daukar hankalin mutane kuma da dama sun bayyana cewa suma suna so suji amsar wannan tambaya daga bbchausa.

Shin da gaske bbchausa basu da amsar wannan tambayar kamar yanda Jabir ya zarga?.

Ko kuwa zasu bashi mamaki su amsamai tambayarshi?.

Zadai mu jira mu gani ya zata kasance.

No comments:

Post a Comment