Wednesday, 27 September 2017

Wasannin zakarun turai: Hotunan da suka dauki hankula daga wasannin da aka buga jiya

A jiya talatane aka buga wasannin kwallo na cin kofin zakarun turai tsakanin gungiyoyi 18, daya daga cikin wasan dayafi daukar hankali shine wanda aka buga tsakanin kungiyar Real Madrid dake rike da kofin da kunguyar kwallo ta Dortmund, a karshen wasan Madrid ta lallasa Dortmund da ci 3-1, wannan hoton na sama dake nuna Bale da Ronaldo wadanda sune sukaci kwallayen, suna murna ya dauki hankulan mutane sosai domin kuwa ya birge.A wannan hoton na sama Pepe da Ricardo Quarezmane rike da kugunansu babu riga bayan da kungiyarsu ta Besiktas itama ta samu nasara akan abokiyar karawarta Leipzig da ci 2-1, wannan hoton nasu shima ya ja hankulan mutane inda aka rika yiwa musamman Pepe tsiya.

Ga hoton cikakken yanda sakamakom wasannin na jiya suka kasance.


No comments:

Post a Comment