Friday, 15 September 2017

Wasu matasa a garin Kano sun sanya kayan Inyamurai suna zagaya gari dan nuna cewa babu maganar tashin hankali

Wannan hotunan wasu matasane a garin Kano da suka sanya kaya irin na al'adar garin Inyamurai suna kida sun zagaya gari a wata alama dake nuna cewa akwai zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin inyamurai da hausawan Jihar, Wannan yana faruwane a daidai lokacin da ake samun rahotannin ciwa al'ummar Hausawa mutunci harma da kisa a can yankin kudanci kasarnan, yankin Inyamuran.Wannan dai abin yabone domin kuwa tashin hankali bashi da rana ko amfani banda asarar dukiya da rayuka babu abinda yake jawowa kuma abinda zaman lafiya be bayarba tashin hankali bazai bayarba.

Allah ya kara hada kan al'ummar kasarnan ya kuma bamu zaman lafiya. Amin.

No comments:

Post a Comment