Friday, 8 September 2017

Wayoyi goma da suka fi sauran wayoyin hannu tsada a Duniya

Wayayoyin hannu sun kasance abokan rayuwa a wannan zamani, kusan ta zamarwa mutane abin dole tunda zatayi abubuwa cikin sauki fiye da ace mutum ya tashi yaje ya aikata da kanshi, a duk shekara kamfanonin wayoyi na gasar fitar da sabbin wayoyin hannu dan yin daidai da zamani, to saidai wasu wayoyin nada dan karen tsada kuma su ba kyauba, idan ma baka saniba ko kyauta aka baka wasu daga ciki ba zaka amsa ba. Ga wayoyin guda goma da sukafi sauran wayoyi tsada a Duniya.

zamu fara lissafi daga kasa;

Ta goma itace Veru Signature Diamond.
World's Top 10 Expensive Mobile Phones in 2017 Vertu Signature Diamond
Ita wannan waya 'yar firit da kuke ganin hotonta a sama an mata kwalliya da kyawawan Lu'ulu'u guda 200 a jikinta kuma ana sayar da ita akan zunzurutun kudi dalar amurka dubu tamanin da takwas, wannan kudin sun kai kwatankwacin sama da naira miliyan talatin a kudin Najeria.

Waya ta tara itace Iphone Princess Plus.
 World's Top 10 Expensive Mobile Phones in 2017 iPhone Princess Plus
Wannan wayar itama tasha ado da kyawanwan Lu'ulu'u guda 180 kuma ana sayar da ita akan zunzurutun kudi har dalar Amurka dubu dari da saba'in da shida da dari hudu, idan aka juya kudin zuwa nairar Najeriya zasu bada fiye da miliyan sittin kenan.

Waya ta takwas itace Black Diamond VIP Smart Phone.
World's Top 10 Expensive Mobile Phones in 2017
Kanfanin Sony Ericsonne ya kera wannan wayar itama wanna wayar tasha kwalliya da Lu'ulu'u kuma tana da matukar kyan fuskar waya duk dadai ba wani girman azo a gani garetaba, ana sayar da ita akan zunzurutun kudi dalar amurka dubu dari uku wanda yayi daidai da sama da miliyan dari a kudin Najeriya.

Waya ta bakwai itace Vertu Signature Cobra.
World's Top 10 Expensive Mobile Phones in 2017 Vertu Signature Cobra
Itama wannan waya wani me harkar kayan kyale-kyale da kwalliyane dan kasar faransa ya kerata, kuma an yi mata kwalliya da wani zanen maciji daya kewa jikin wayar, haka kuma wayar tasha ado da lu'ulu'u da yakutu da sauran kayan ado na alfarma itama kuma ana sayar da ita akan kudi dalar Amurka dubu dari uku wamda suke dai-dai da sama da naira miliyan dari.

Waya ta shida itace Gressor Luxor Las Vegas Jackpot.

World's Top 10 Expensive Mobile Phones in 2017 Gresso Luxor Las Vegas Jackpot
Wannan wayar an yita da tsantsar Zinarene, babu hadi, haka kuma bayanta an yishi da wani katakone na musamman da ake samu a nahiyar Afrika wanda yakai kusan shekaru dari biyu a Duniya, kuma shine katako mafi tsada a Duniya haka kuma madannanta an yi sune da wani gilashi me dan karan tsada, ana sayar da wannan wayar akan kudi dalar Amurka miliyan daya wanda a kudin Najeriya sun kai kwatankwacin fiye da naira miliyan dari uku da hamsin.

Waya ta biyar itace Diamond Crypto SmartPhone.
 World's Top 10 Expensive Mobile Phones in 2017 Diamond Crypto Smartphone
Itama wannan waya tasha ado da kalar Zinare daban-daban kuma wadanda suka kerata sunce tana bayar da kariya da taimakawa wajen kar ayi garkuwa da mutum da kuma wajan batawa mutum suna ha hanyar zamani. Ana sayar da wannan waya akan zunzurutun kudi dalar Amurka miliyan daya da dubu dari uku wanda yayi daidai da kwatankwacin kudin Najeriya sama da naira miliyan dari hudu da sittin.

Waya ta hudu itace GoldVish Le Million.
  
World's Top 10 Expensive Mobile Phones in 2017 GoldVish-Le-Million
Itama wannan waya wani me harkar kayan kyale-kyalene ya kerata kuma tasha ado da Zinare da lu'ulu'u wayar ta taba shiga kundin tarihin abubuwan bajinta na Duniya a matsayin wadda tafi kowace waya tsada kuma itama ana sayar da ita akan zunzurutun kudi dalar Amurka miliyan daya da dubu dari uku wanda yayi daidai da kwatankwacin kudin Najeriya miliyan dari hudu da sittin.

Waya ta uku itace Iphone 3G king's Button.
    World's Top 10 Expensive Mobile Phones in 2017 iPhone 3G King’s Button
Wannan waya itama tasha ado da zinare me yawa wanda kusan shine yasa tayi dan karen shada ake sayar da ita akan zunurutun kudi dalar Amurka miliyan biyu da dubu dari hudu wanda sukayi daidai da kwatankwacin kudin Najeriya Miliyan dari takwas da sittin, itama wani gwanin harkar kayan alatune ya kerata.

Waya ta Biyu itace Supreme Goldstriker Iphone 3G 32GB.
World's Top 10 Expensive Mobile Phones in 2017 Supreme Goldstriker iPhone 3G 32GB
Wanan waya tasha ado da tsabar zinare da lu'ulu'u da sauran kayan alatu da ake ji dasu a Duniya kuma ana sayar da ita akan zunzurutun kudi dalar Amurka miliyan dari uku da dubu dari biyu wanda yayi daidai da kudin Najeriya kwatankwacin sama da naira biliyan daya da dubu dari da hamsin.

Waya ta daya da tafi kowace waya tsada a Duniya itace  Diamond Rose Iphone 4 32GB.
World's Top 10 Expensive Mobile Phones in 2017 Diamond-Rose-iPhone
Wannan waya me suna Iphone 4 Diamond Rose itace wayar da tafi kowace waya tsada a Duniya kuma tasha ado da kala-kalar zinariya da lu'ulu'u masu yawan gaske, ana sayar da wannan waya akan zunzurutun kudi dalar Amurka miliyan takwas wanda daidai yake da kwatankwacin kudin Najeriya sama da Naira Biliyan biyu da miliyan dari da saba'in.

No comments:

Post a Comment