Wednesday, 27 September 2017

"'Yan fim da mawaka sunfi shugaba Buhari suna a idon Duniya">>inji sanata Ben Bruce

Sanata Ben Bruce daya fito daga yankin kudancin kasarnan ya bayyana cewa ya shiga gurare daban-daban a Duniya amma abinda ya fahimta shine mawakinnan wato Fela da kuma shahararrun 'yan fim dinnan na yankin kudu wato Omotola Jalade da Geneveive Nnaji sunfi Shugaban kasa Muhammadu Buhari yin suna a tsakanin mutanen Duniya haka kuma ya kara da cewa mutanen Duniya sunfi sanin Najeriya da wadancan shahararun mutane fiye da cewa Najeriyar nada arzikin man fetur.

Sanata Ben Bruce wanda dan jam iyyar adawa ta PDP ne ya bayyana hakane a dandalinshi na sada zumunta da Muhawara dake shafin Twitter, wasu sun yarda da wannan batu nashi yayin da wasu sukace sam ba gaskiya bane domin kuwa kowace kasa da sunan shugaban ta aka santa, kumama farin jinin shugaba Buhari na musammanne, kawai dai zafin adawane yasa Ben Bruce fadin wannan magana.

Mawaki Fela.
Fitacciyar jarumar finafinan kudu Geneveive Nnaji.
Fitacciyar jarumar finafinan kudu Omotola Jalade.

No comments:

Post a Comment