Friday, 22 September 2017

Yanda taron karrama matan Arewa ya kasance

Fitacciyar Jarumar finafinan Hausa Hadiza Gabon da Fati Nijar da Hauwa Maina da Abbas Sadik sun halarci gurin taron karrama matan Arewa da wata kungiya ta shirya yi a garin Kaduna, taron dai wanda a farko akayi niyyar yinshi a Hotel 17 amma daga baya saboda wasu dalilai da masu shirya taron kadai suka sani suka mayar dashi  Kabir Gymnasium. Jama'a da dama da suka hada da masu nishadantarwa da 'yan fim da mawaka da masu sarauta da masu mukaman siyasa sun halarci gurin taron.

Hutudole.com ya dauko muku yanda wasu fitattun fuskoki suka haskaka a gurin.
Anan shahararriyar mawakiyar Hausace Fati Nijar tare da Abokanta a gurin taron.
Anan Hauwa Maina ce a gurin taron.
Anan fitaccen jarumin fim din Hausa ne Abbas Sadik dake gudanar da harkar taron.
Hajiya Halima Idris me baiwa gwamnan jihar Kaduna shaawara akan harkokin kirkire-kirkire ta halarci gurin taron, tana daya daga cikin matan da sukayi jawabi a gurin kuma aka karramasu da lambar yano.
Saidai manyan matan da aka gayyata kamar yanda yake a cikin sanarwar taron ba duka suka samu halartaba irinsu matar shugaban kasa A'isha Buhari da dai sauransu.

No comments:

Post a Comment