Sunday, 10 September 2017

Za'a karrama fitattun matan Arewa

An shirya karrama matan Arewa da sukayi fice ta fannoni daban-daban, musamman ta bangaren shugabanci, shirin  karramawar wanda za'ayi a garin kaduna ranar 22 ga watan Satumba da muke ciki zai karrama fitattun matan Arewa da dama wanda mafi yawancinsu matan shuwagabannine da kuma 'yan siyasa har ma da jaruman finafinan Hausa, daga cikinsu akwai matar shugaban kasa, Hajiya A'isha Muhammad Buhari da ministar harkokin mata, Sanata A'isha Alhassan da matar shugaban majalisar dattijai Toyin Saraki.Akwai kuma matan tsofaffin shuwagabanni da matan gwamnonin Arewa, daga ciki akwai mata uku daga masana'antar finafinan Hausa Rahama Sadau da Hadiza Gabon da Jamila Umar (Nagudu).

A wani abu me ban mamaki, ganin cewa karramawar ta matace sai gashi an samu maza biyu da suma za'a karramasu cikin tsakiyar matan, mutanen kuwa sune gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma gwamanan jihar Adamawa Sanata Bindo Jibirilla.

Allah ya kaimu wannan  rana lafiya kuma muna taya wadanda za'a karrama da wadannan kyautuka murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment