Wednesday, 25 October 2017

"Abin Kunya: Ko mu dake zaune a kasar Amurka ba za mu yi irin wannan (shigar ba)">>wata ta gayawa Jamila Nagudu

Saka wannan hoton nata sanye da jajayen kaya, abin wuya me kyau tasha jan baki gashi kuma tasha irin kwalliyarnan ta zamani saidai kanta babu dankwali, fitacciyar jarumar finafinan Hausa Jamila Umar(Nagudu) tasha ruwan Allah wadai da kiranye-kiranye cewa wannan hoto nata bai dace ba, daya daga cikin mabiyanta a dandalin sada zumunta da muhawara ta gaya mata cewa ko su da ke zaune a kasar Amurka ba za su yi irin wannan abin da Jamilar ta yi ba dan "sun fita tsoron Allah".

Idan mutum bai yi daidai ba to baiyi daidai ba amma maganar "tsoron Allah a zuciya yake", shi kadai yasan wana yafi jin tsoronshi, duk da yake cewa mu mutane mukan yiwa mutum fassara da irin yanayin rayuwar da mutum keyi ta zahiri kawai.

Gadai abinda matar tace kamar haka:

"(Wannan ne) hoto mafi muni (dana taba gani)...........(Wannan) abin kunaya ne.......ko mu dake zaune a kasar Amurka mun fiki tsoron Allah......yanzunnan zan daina bibiyarki(a dandanlinki na sada zumunta).

No comments:

Post a Comment