Sunday, 29 October 2017

Abin mamaki: Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya hau jirgin fasinja

A lokacin da masu kudi da masu rike da madafin iko, irin su gwamnoni duk lokacin da suka tashi yin tafiya suke daukar hayar jirgin sama ko kuma su hau nasu na kashin kansu da iyalansu, an ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a cikin jirgin fasinja dake cike da mutane shi da matarshi, rahotanni sun bayyana cewa gwamnan yana dawowa daga jihar Imo ne zuwa gida Kano.Wasu sun yabamai da wannan abu da yayi inda suka bayyana cewa dama shugaba be kamata yana gujewa mutane ba.No comments:

Post a Comment