Saturday, 28 October 2017

Abin mamaki: Jirgin sama yayi karo da tsuntsu ya lotse

Wannan wani jirgi ne da labarinshi ya dauki hankulan mutane duk da da yawa basu yarda da labarin ba suna ganin cewa bazai yiyu ba, idan aka kalli goshin jirgin za'a iya ganin ya lotse, me magana da yawun kamfanin jirgin ya bayyana cewa suna tsammanin jirgin yayi karo da wani tsuntsune lokacin da yake kokarin sauka amma fasinjoji sun sauka lafiya, babu wanda yaji rauni saidai jirginne ya lotse.Mutanen da suka yi sharhi akan wannan labarin sun rika rubutu cikin barkwanci suna fadin anya kuwa wannan tsuntsu ne ko dai 'yan sama jannatine jigin yayi karo dasu, ko kuwa wane irin jiki tsuntsu gareshi da har zai lotsa jirgi haka?

No comments:

Post a Comment