Sunday, 15 October 2017

Abin mamaki:Bata san tana dauke da cikiba sai awanni hudu kamin ta haihu

Wani abin mamaki ya faru da wata  matashiya a kasar Ingila me suna Connie Whitton, 'yar shekaru goma sha tara da haihuwar tace bata san tana dauke da cikiba har sai da ya rage awanni hudu kamin ta haihu. Yarinyar gwanar daukar hotunace tana sakawa a dandalinta na sada zumunta, kuma bata son tayi kiba, kwatsam sai taga ta fara nauyi da yin kiba kuma taji ta fara jin ciwon baya mai tsanani, wata rana bayan ta dawo daga gurin fati inda tayi mankas da giya sai ta zauna cikin kunci da bacin rai, da mahaifiyarta taga haka saita tambayaeta.Nan kuwa ta zayyanawa mahaifiyarta ta abinda ke damunta. Da mahaifiyar tata taji haka saita shawarceta ta tafi asibiti.

Taje Asibiti aka mata gwaje gwajen cututtuka amma bata da ko daya amma sai aka gano tana dauke da juna biyu, nan ta cika da mamaki, awanni hudu bayan hakan sai ta haifi danta namiji.

Ta kara gayawa manema labarai cewa ita kwata-kwata bataji wata alamar cewa tana dauke da cikiba in banda nadan awanni hudunnan.

Lallai Allah me iko

No comments:

Post a Comment